Daga Jabir Ali Dan Abba

Shugaban karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da ‘Ogan Boye’ ya amince da nadin mataimaka na musamman guda 60 da za su yi aiki a ɓangarori daban-daban a karamar hukumar.

A cewar takardar amincewa da sakataren karamar hukumar, Ado Muhammad Hotoro ya sanya wa hannu, nadin na daya daga cikin kokarin da shugaban karamar hukumar ya ke yi na bunkasa da aiyuka don ci gaban kananan hukumomi.

Jerin sunayen wadanda aka nada sun hada da masu bayar da rahoto na musamman guda 18 da aka ba su don kula da sassa daban-daban, kasuwanni, da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a cikin karamar hukumar.

Daga cikin hadiman nasa harda Ahamad Sunusi Aminu Imam ,a matsayin maitaimakawa Ogan takan harkokin cikin gida

Wasikar ta kuma kara jaddada cewa an yi nadin ne bisa cancanta, sadaukarwa, gaskiya, da jajircewa, wanda ke nuni da manufar gwamnati na samun ingantaccen shugabanci.

Har ila yau, ta bayyana kwarin gwiwar cewa wadanda aka nada za su yi aikin da aka ba su da himma domin tallafa wa manufofin ci gaban kananan hukumomin.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version