Shugaban karamar hukumar Gwale Hon. Abubakar Ma’azu (Mojo) ya tallafawa masu Sana’ar dinka rariya a yankinsa da jari domin karfafa musu guiwar dogoro da kansu.

Mojo wanda ya bada gudun mowar kudi naira dubu 500 ga masu Sana’ar dinka rariyar ,ya jinjina musu abisa yadda suke dogaro da kansu lokacin da yakai musu ziyara a wajen Sana’arsu dake Gwale filin Mushe.

A cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban karamar hukumar ta Gwale akan harkokin yada labarai a zamanance Saminu Shuaibu Saminu Cisse ya fitar,wanda Jaridar TST Hausa ta samu kofi,Hon Mojon yace zaici gaba da tallafawa masu karamar Sana’a a Gwale domin dogoro da kansu musamman matasa maza da mata.

Ya tabbatarwa masu dinka rariyar cewa , karamar hukumar zata ci gaba da tallafa musu a koda yaushe.

Sannan yaja hankalin matasa da su daina raina Sana’a komai kankantar ta.

Yace wannan Sana’a ta dinka rariya, Sana’a ce wacce ta samo asali a Kano,dan haka ,Mojo yace karamar hukumar zata bada goyon baya domin ganin an horos da matasa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version