Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da kammala aikin hajjin shekarar 2026 tare da bayyana samun nasarar gudanar da aikin Hajjin shekarar 1447 Hijiriyya da ta yi daidai da 2026 Miladiyya, bayan kammala mafi yawan muhimman ibadun Hajji cikin tsari da kwanciyar hankali.

Mataimakin Sarkin Yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal, ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar daga Mina a ranar Juma’a, inda ya yaba da kokarin hukumomi da jami’an da suka gudanar da ayyuka domin tabbatar da tsaro, lafiya da walwalar miliyoyin Alhazai da suka halarci aikin Hajjin bana.

Ya ce an samu nasarar tafiyar da harkokin zirga-zirgar Alhazai tsakanin Mina, zuwa Arafah da Muzdalifah cikin sauki, tare da samar da ingantattun ayyukan lafiya, tsaro da agaji a dukkan wuraren ibada masu tsarki.

Yarima Saud bin Mishaal ya bayyana aikin Hajjin bana a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen Hajji mafi inganci, yana mai cewa hadin kai tsakanin jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki ne ya taimaka wajen samun wannan nasara.

Haka kuma ya yaba da kokarin jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya, masu aikin sa-kai da sauran hukumomin da suka yi aiki dare da rana domin tabbatar da jin dadin bakin Allah da suka zo daga sassa daban-daban na duniya.

Sauddiya ta kuma ce zata maida hankali domin tunkarar aikin hajjin 2027 tare da fatan samun nasara

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version