Gwamnatin Saudiyya ta fitar da sabon jadawalin shirye-shiryen Hajjin shekarar 2027 tare da gabatar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin ƙara inganta hidimomin da ake bai wa Mahajjata da kuma sauƙaƙa gudanar da aikin Hajji.

Sabbin tsare-tsaren sun haɗa da amfani da tsarin fasahar sadarwa wajen gudanar da harkokin Hajji, inda aka tanadi cewa za a riƙa gudanar da dukkan kwangilolin hidimar Hajji ta hanyar manhajar Nusuk, yayin da biyan kuɗaɗe zai kasance ta tsarin walat na lantarki (e-wallet).

Haka kuma, Saudiyya ta sanya wasu sabbin ƙa’idoji da suka shafi kula da lafiyar Mahajjata, inda aka tanadi samar da likitoci da ma’aikatan jinya kusan guda biyar ga duk yawan Mahajjata 1,000 domin tabbatar da ingantacciyar kulawar lafiya a lokacin aikin Hajjin na 2027.

A bana yawan Alhazai miliyan 1 da dubu dari, 7 ne suka sauke farali a Saudiyya.

A zantawarsa da manema labarai a birnin Makkah Ministan kula da Hajji da Umrah na kasar Indonesiya,kasar da tafi kowacce kasa yawan Alhazai a aikin Hajjin bana wato Mochamad Irfan Yusuf, ya bayyana cewa ƙasarsa wacce ta karbi wannan sabon tsarin daga Saudiyya yace za su daidaita shirye-shiryen da ake bukata ya yi daidai da sabon jadawalin da Saudiyya ta fitar.

TST Hausa ta rawaito cewa sama da Mahajjata dubu 200 ne suka je Saudiyya daga kasar ta Indonesiya.

Ya ce gwamnatin Indonesiya za ta yi nazari sosai kan yadda za ta aiwatar da sabon tsarin, musamman ma dangane da batun amfani da kamfanin hidimar Hajji guda ɗaya, ganin cewa ƙasar na daga cikin waɗanda ke da mafi yawan Mahajjata a duniya duk shekara.

Ya ƙara da cewa sabbin tsare-tsaren na buƙatar ƙasashe su fara shirye-shiryensu tun da wuri domin cika dukkan sharuddan da aka gindaya kafin fara ayyukan Hajjin 2027.

Masana harkokin Hajji na ganin cewa waɗannan sauye-sauye na nuna ci gaba da ƙoƙarin Saudiyya na amfani da fasahar zamani da sabbin hanyoyin gudanarwa domin ƙara inganta ayyukan Hajji, da tabbatar da samun sauƙi, tsaro da walwalar Mahajjata daga sassa daban-daban na duniya.

Ana sa ran sabbin tsare-tsaren za su zama wani muhimmin mataki wajen ƙara inganta yadda ake gudanar da ibadar Hajji a shekaru masu zuwa, musamman ta fuskar hidima, kula da lafiya da kuma amfani da tsarin zamani wajen gudanar da harkokin Mahajjata.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version