An shiga jimami a Jihar Sokoto bayan da aka tabbatar da rasuwar wasu mahajjata biyu daga jihar a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya bayan sun kammala muhimman ibadun Hajjin bana na shekarar 2026 suna shirin dawowa gida.
Mai magana da yawun hukumar kula da jin dadin Alhazan jihar Sokoto Faruku Umar,ne ya shaida hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda yace mataimakin Amirul Hajja na jihar Sokoto wanda shine Grand Khadi na jihar wato Alhaji Sodangi Acida ne ya sanar da mutuwar Alhazan a zantawarsa da manema labarai a birnin na Makka.
Yace Alhazan sun hada da Hajiya Ladi Umar daga karamar hukumar Bodinga da Hadiza Umar daga karamar Hukumar Yabo a Sokoton.
Hukumar kula da aikin Hajji ta jihar da sauran jami’an da ke kula da alhazan Najeriya a ƙasa mai tsarki sun bayyana alhini kan rasuwar mahajjatan, tare da jajanta wa iyalansu da al’ummar jihar Sokoto baki ɗaya.
Kamar yadda dokokin ƙasar Saudiyya suka tanada, an gudanar da jana’izar mamatan tare da binne su a ƙasa mai tsarki bayan kammala dukkan matakan da suka dace.
Rasuwar mahajjatan ta sake tunatar da al’umma cewa aikin Hajji ibada ce mai ɗauke da ƙalubale na jiki, musamman ga tsofaffi da masu fama da wasu matsalolin lafiya
Duk da haka, Musulmai da dama na kallon rasuwa a ƙasa mai tsarki bayan gudanar da Hajji a matsayin wata falala daga Allah Maɗaukakin Sarki.
Al’ummar Sokoto da sauran Musulmai na ci gaba da addu’ar Allah Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya karɓi ibadunsu, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu.
TST Hausa ta rawaito cewa ana sa ran fara dawo da Alhazan na Sokoto gida Najeriya a ranar 14 ga watan Yuni kamar yadda Amirul Hajj din ya sanar.
