Yawan marasa aikin yi a Najeriya ya ragu zuwa kashi 4.3 cikin dari watanni hudu na tsakkiyar shekarar 2024, lamarin da ke nuni da cewa an samu ingantuwar aikinyi a Najeriya.
Dangane da sabon rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar ya nuna raguwa daga kashi 5.3 cikin dari da aka fitar cikin watanni hudu na farkon shekarar 2024 kuma yana nuna murmurewa a hankali daga kashi 5.0 a cikin dariba watanni hudu na karahen 2023.
Rahoton ya nuna cewa an samu yawaitar aikin karfi da ya karu da kashi 79.5 cikin ɗari, daga kashi 77.3 cikin ɗari a watanni hudu na farkon shekarar 2024.
Jaridar TST Hausa ta rawaito cewa watakila hakan na da nasaba da yadda yan Najeriya suka rungumi aikin karfi fiye da aikin gwamnatin.
Aikin karfin a Najeriya acewar rahoton ya karu zuwa kashi 78 cikin dari
2 Comments
This is good website to us
Thanks very much