Kungiyar kwadago ta birnin tarayya Abuja ta umurci ma’aikatan birnin baki dayansu da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 1 ga Disamba, 2024.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar NLC na Abuja Stephen Knabayi.
Idan za’a iya tunawa kungiyar NLC ta umurci ma’aikata a jihohi 14 da kuma babban birnin tarayya Abuja da su fara yajin aikin daga ranar Lahadi 1 ga watan Disamba kan rashin aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Yan kwadagon sunce har yanzu sun kasa cimma yarjijeniyar fara biyan mafi karancin albashin da ministan Abuja Nyenson Wike