Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, na cigaba da fuskantar matsin lamba mai karfi daga manyan jami’an gwamnati domin ya ajiye mukaminsa.

Mataimakin gwamnan na fuskantar matsin lambar ne bayan ya ki bin sahun Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Yanzu haka daga majalisar dokokin kano ana cigaba da tattaunawa a tsakanin ‘yan majalisar da ke goyon bayan gwamnan kan yiwuwar fara shirin sauke mataimakin gwamnan idan ya ki yin murabus da kansa.

Sai dai wani babban jami’i a ofishin mataimakin gwamnan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ubangidansa ba shi da niyyar yin murabus sai dai idan Sanata Kwankwaso ne ya umurce shi.

A halin da ake ciki kuma, majalisar dokokin jihar Kano ta ce babu wani batu a hukumance da aka gabatar gabanta dangane da shirin sauke mataimakin gwamnan.

Mai magana da yawun majalisar, Kamal Shawai, ya ce majalisar na hutu ne a halin yanzu, kuma ba za ta dawo zamanta ba sai a watan Fabrairun 2026.

Kamal Shawai ya bayyana cewa ko da yake ‘yan majalisa sun tattauna batutuwan da suka shafi sauya shekar gwamnan a tsakaninsu ba a hukumance ba, babu wata takarda ko kuduri da aka gabatar wa majalisar dangane da neman mataimakin gwamnan ya sauka ko a saukeshi.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version