Jam’iyyar APC mai mulkin kasa tace jam’iyyar adawa ta PDP matsayinta na jam’iyya wacce sannu a hankali ke rugujewa kowa ya kama gabansa ,amma acewar APCn a haka PDP ke kwadayin dawowa mulkin Najeriya a shekarar 2027.
Jam’iyyar ta APC ta bukaci ‘yan Najeriya da su tabbatar da cewa PDP ba ta dawo kan karagar mulki ba sakamakon yadda ta lalata makomar Najeriya a shekaru 16 data shafe tana mulki a baya.
Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Bala Ibrahim ne ya yi wannan roko a wata hira da jaridar PUNCH.
Yace har Yanzu yan Najeriya basu warke daga mulkin zaluncin da PDP tayi daga shekarar 1999 zuwa 2015 ba.
APCn tace jam’iyya kamar PDP da bata iya mulkar kanta ba , kuma ace itace zata sake dawowa ta mulki kasa kamar Najeriya.
Yace akwai rikice rikice da yawa a cikin PDP da ba zata iya gyarawa ba kafin zaben 2027.
A halin da ake ciki dai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar bai halarci taron sasanta rikicin cikin gida da manyan jiga-jigan jam’iyyar PDPn na shiyyar Arewa maso Gabas suka shirya a jihar Bauchi inda suka tattauna kan kokarin sasantawa da dabarun jam’iyyar.
Taron wanda aka gudanar a ranar Alhamis, ya samu halartar gwamnonin PDP uku na yankin.
Gwamnonin sun hada da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, wanda kuma shine Shugaban Kungiyar gwamnonin PDP na Najeriya da takwaransa na Taraba Dr Agbu Kefas, dana jihar Adamawa Governor, Ahmadu Fintiri.