Daga Kabiru Muhammad Getso

Hukumar Bunƙasa Harkokin Noma da Samar da Abinci ta Jihar Jigawa (JATA) ta musanta rahotannin da ke yawo cewa gwamnatin jihar na sayar da kayayyakin noma daidai da farashin kasuwa, tana mai bayyana cewa har yanzu ana sayar wa manoman jihar kayayyakin aikin noma cikin rangwamen farashi domin ƙarfafa noman zamani.

Babban Daraktan Hukumar, Dr. Saifullahi Umar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishinsa da ke Birnin Dutse.

Ya ce ikirarin da wasu ke yaɗawa cewa an ɗaga farashin kayayyakin noma zuwa daidai da na kasuwa ba gaskiya ba ne, yana mai bayyana irin wannan batu a matsayin jita-jita marar tushe da makama.

Dr. Saifullahi ya jaddada cewa manufar gwamnatin Jihar Jigawa ita ce sauƙaƙa wa manoma hanyoyin samun kayan aikin noma a farashi mai rahusa domin bunƙasa noma, ƙara yawan amfanin gona da kuma tabbatar da wadatar abinci a faɗin jihar.

Ya yi kira ga manoma da daukacin al’ummar Jigawa da su yi watsi da duk wani rahoto mara inganci da ake yaɗawa, tare da tabbatar musu cewa gwamnatin jihar ba ta sauya tsarin rangwamen da take bai wa manoma ba.

Babban Daraktan ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa Gwamna Malam Umar Namadi cikakken goyon baya da haɗin kai domin gwamnatin ta samu damar ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen bunƙasa noma da sauran ayyukan ci gaban al’umma a faɗin Jihar Jigawa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version