Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta sanar da tura sama da ma’aikatan lafiya 52,000 domin kula da lafiyar alhazai yayin gudanar da aikin Hajjin 2026 daga zafin rana musammam a lokacin Arfa.

Rahotanni sun bayyana cewa an baza jami’an lafiyar ne a wurare daban-daban na aikin Hajji da suka hada da Makkah, Mina, Arafat da Muzdalifah domin tabbatar da bayar da kulawar gaggawa da sauran ayyukan lafiya ga miliyoyin alhazai da ake sa ran za su halarci aikin Hajjin bana.

Matakin na zuwa ne yayin da hukumomin Saudiyya suka fitar da gargadi kan matsanancin zafi da ake fuskanta a wuraren aikin Hajji, inda yanayin zafin ya kai kusan digiri 48 a ma’aunin Celsius a wasu yankuna.

Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa ma’aikatan lafiyar da aka tura sun hada da likitoci, jami’an jinya, kwararrun masu kula da masu fama da bugun zafin rana da kuma jami’an agajin gaggawa da aka tanada domin daukar matakin gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Saudiyya ta kuma kara yawan cibiyoyin lafiya da motocin daukar marasa lafiya tare da samar da kayan aikin zamani domin tabbatar da lafiyar alhazai a dukkan matakan aikin Hajjin.

Baya ga haka, an kara daukar matakan kariya domin rage illar tsananin zafi, ciki har da fadada wuraren inuwa, inganta tsarin sanyaya iska a tantunan Mina da kuma samar da ruwan sha a wurare daban-daban da alhazai ke taruwa.

Masana harkokin lafiya sun yi gargadin cewa tsofaffi da masu fama da wasu cututtuka na daga cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin matsalolin da zafi ka iya haifarwa, saboda haka aka bukaci alhazai da su rika kula da lafiyarsu tare da bin umarnin jami’an lafiya a lokacin gudanar da ibadar Hajji.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version