Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa ba zai tsorata da duk wani yunƙuri na ƙwace masa mulki a zaɓen shekarar 2027 ba.

Tinubu ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya karɓi bakuncin mambobin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na da ƙuduri na fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci da jahilci, tare da tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya a ƙasar.

Ya buƙaci ‘yan ƙungiyar da su yi aiki wajen gina ƙasa mai haɗin kai da manufa guda, yana mai cewa ci gaban ƙasa ba zai yiwu ba sai da haɗin kai da bin tsarin dimokuraɗiyya.

Tinubu ya kuma soki ɓangaren ‘yan adawa, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta amince da rashin bin doka da oda ba, tare da jaddada muhimmancin mutunta hukuncin kotu da raba iko a gwamnati.

A wani ɓangare na jawabin, ya yi ishara ga taron jam’iyyar ADC, yana mai cewa ba zai bari “hayaniya ko rashin tsari” su firgita shi ba.

Ya ƙara da cewa waɗanda ke ƙoƙarin karɓar mulki daga gare shi ba za su iya firgita shi ba, yana mai cewa ya riga ya saba da irin wannan fafatawa a siyasa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version