Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana farin cikinsa kan dawowar tsohon Gwamna kuma Sanata, Ibrahim Shekarau, zuwa jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan wani babban ci gaba ne da zai kara dankon karfin jam’iyyar a jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa dawowar Shekarau na daga cikin muhimman matakai na kara hada kai da karfafa APC a Kano.
Ya kara da cewa ana kan tattaunawa da sakatariyar jam’iyyar ta kasa domin fitar da ranar da za a gudanar da bikin tarbar tsohon Gwamnan a hukumance cikin APC.
Gwamnan ya jaddada cewa APC na ci gaba da samun karuwar goyon baya daga al’umma, lamarin da ke kara tabbatar da matsayinta a matsayin babbar jam’iyya mafi tasiri a siyasar Kano.
A cewarsa, jam’iyyar na cikin cikakken shiri domin tunkarar zabuka masu zuwa, tare da kudurin lashe dukkan mukaman da za a fafata, yana mai danganta hakan da hadin kai, kyakkyawan tsari da kuma dabarun siyasa da aka shimfida.
Har ila yau, ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar da magoya baya cewa shugabancin APC a jihar ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kara karfafa hadin kai a cikin gida, tare da fadada gindin goyon baya daga tushe har zuwa sama.
Gwamna Yusuf ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan jam’iyyar da su ci gaba da tsayawa tsayin daka, su kara zage damtse wajen jan hankalin jama’a da wayar da kai, domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabukan da ke tafe.
TST Hausa ta rawaito cewa a shekarar 2018 ne Malam Shekarau ya fice daga PDP ya koma APC daga baya ya sake ficewa daga APC ya koma PDP Yanzu ya sake komawa APC
