Kwamishinan kasuwanci na jihar Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi yace a tarihin Siyasar Kano ba’a taba samun wanda yasha zagi sama dashi ba.
Shehu Wada Sagagi wanda ya rike mukamin Shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Kano tsawon shekara daya da rabi , gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke Shehu Sagagin da Sakataren gwamnati da kwamishinoni biyar ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2025.
Daga baya ne Gwamna Yusuf ya sake nada Sagagi a matsayin kwamishinan ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta Kano.
A wata hira da Rahma Radio ciki Shirin labaran karshen mako kashi na biyu kan abinda ya shafi ma’aikatarsa ,Wada Sagagi yace ba’a taba samun dan yasa da yasha zagi sama dashi ba a Kano.
Yace lokacin da ya rike Shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin kano,ana ganin Kamar shine ya hana ruwa gudu,kuma komai akayi na rashin daidai shi ake dorawa laifi.
Wannan tasa nayi bikin jini ,ake ta zagina-inji Sagagi.
Saidai tsohon Shugaban ma’aikatan na gidan gwamnatin Kano ,Wada Sagagi yace ya yafewa duk masu zaginsa ,saboda shima yanaso Ubangiji ya yafe masa.
Yace a matsayinsa na kwamishinan kasuwanci,ya hada kai da ma’aikatun gwamnati a kalla 7 domin bunkasa kasuwanci a Kano.
Ma’aikatun da yace sun hada da kai da su sun hada da Ma’aikatar noma da ma’adanai da makamashi da ta kasafin kudi da ta Muhalli da ma’aikatar sufuri da ma’aikatar Kasa da hukumar karbar haraji.
Daga nan kwamishinan yaci alwashin farfado da masana ‘antun Kano da suka durkushe saboda karancin lantarkin da kuma wasu Sana’oin gargajiya
Yace gwamnatin Kano zata karfafawa ma’aikatar makamashi guiwa domin samar da lantarkin ga masana ‘antun da suka daina aiki.