Hukumar gudanarwar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi ta dakatar da wasu malamai guda bakwai bisa zargin cin zarafin ɗalibai ta hanyar neman lalata da kuma sayar da takardun koyo da koyarwa da wasu littattafai ba bisa ƙa’ida ba.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na kwalejin, John Onimisi, ya tabbatar da matakin, yana mai cewa an kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar zarge-zargen.
Shida daga cikin malaman an dakatar da su ne kan zargin tilasta wa ɗalibai sayen takardun handout da littattafai, yayin da aka dakatar da ɗaya bisa zargin neman lalata da wata ɗaliba.
Wasu ɗalibai mata sun yi zargin cewa wasu malamai na neman kuɗi ko lalata da su domin ba su maki ko kuma su tsallake jarabawa.
Haka kuma sun yi zargin cewa an fara sake samun matsalolin ƙungiyoyin asiri da wasu munanan ɗabi’u a harabar makarantar.
Sai dai hukumar makarantar ta ce tuni ta fara ɗaukar matakan ladabtarwa, tare da tabbatar da cewa za ta fitar da sakamakon binciken da zarar an kammala shi.
