Hukumomin kasar Saudiyya sun umurci a fara azumi daga gobe Laraba, 18 ga watan Fabareru na 2026

A yau Talata ne rahotanni ke cewa an ga jinjirin watan azumin Ramadan a sassa daban daban na kasar Saudiyya.

Hukumomi sun umurci a fara azumi daga gobe Laraba.

Shafin Haramain Sharifain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce, “an ga jinjirin watan Ramadan na shekarar 1447 wato shekarar 2026 a Saudiyya.

KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ramadan-gwamnatin-kano-ta-fitar-da-shawarwari-kan-kula-da-lafiya-da-nauin-abincin-da-ya-kamata-a-ci/

Tunda farko babbar kotun Ƙolin Saudiyya ce ta yi kira ga dukkan Musulmi a faɗin ƙasar da su fita domin neman jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 29 Sha’aban 1447AH, daidai da 17 ga Fabrairu, 2026 bisa kalandar Umm Al-Qura.

Sanarwar ta kara da cewa za’a fara Sallar Asham a kasar musamman masallacin Ka’aba da na Madina wato Masallacin Annabi Muhammad SAW.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version