Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA) ta karrama Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Malam Mustapha Muhammad, da kambun “Dan Najeriya na Mako” (Nigerian of the Week), saboda nuna gaskiya da rikon amana bayan ya mayar da Riyal 6,000 da aka yi masa kuskuren biyansu yayin aikin Hajjin bana a Kasar Saudiyya.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa matakin da Mustapha Muhammad ya dauka na mayar da kudin da zarar an gano kuskuren ya zama abin koyi ga masu rike da mukaman gwamnati da sauran ‘yan kasa, musamman a wannan lokaci da ake kokarin kara karfafa amincewar jama’a ga hukumomi da masu gudanar da harkokin mulki.

NOA ta ce kudin, wadanda darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 2.4, an biya su ne bisa kuskure a lokacin gudanar da ayyukan Hajji. Sai dai bayan da aka gano lamarin, ya mayar da dukkan adadin kudin ba tare da jinkiri ba, lamarin da ya nuna cikakken rikon amana da tsoron Allah wajen gudanar da al’amuran da suka shafi dukiyar jama’a.

Hukumar ta jaddada cewa ko da yake wasu na iya ganin adadin kudin ba wani babban abu ba ne, amma ainihin darajar lamarin tana cikin sakon gaskiya da mutunci da ya kunsa.

Sanarwar ta ce:

“Kyawawan dabi’u da mutuncin kowace al’umma suna ginuwa ne daga irin wadannan ayyuka na gaskiya, rikon amana da kishin kasa da mutane ke nunawa a lokacin da suka samu damar zabar abin da ya dace.”

NOA ta kuma yi nuni da cewa kafin shiga aikin gwamnati, Mustapha Muhammad ya yi fice a fannin aikin jarida, inda ya yi aiki a manyan kafafen yada labarai na cikin gida da na duniya da suka hada da THISDAY Newspaper da Bloomberg.

A cewar hukumar, matakin da ya dauka ya yi daidai da kyawawan dabi’un aikin jarida da suka hada da gaskiya, mutunci, daukar alhaki da kuma kare muradun jama’a.

Hukumar ta bayyana cewa zaben sa a matsayin Dan Najeriya na Mako wani bangare ne na kokarinta na yabawa da kuma haskaka mutanen da ke nuna kyawawan dabi’u a aikace, domin su zama abin koyi ga sauran al’umma.

“Ta hanyar wannan karramawa, muna isar da sako ga jami’an gwamnati, ma’aikatan kafafen yada labarai da daukacin ‘yan Najeriya cewa gaskiya, rikon amana, aiki tukuru da daukar alhaki su ne ginshikan gina kasa mai ci gaba da dorewar zaman lafiya,” in ji sanarwar.

Shirin Nigerian of the Week na daga cikin manufofin NOA na bunkasa kyawawan dabi’u da suka kunshi gaskiya, kishin kasa, shugabanci na gari da kuma zama dan kasa nagari, kamar yadda Kundin Darajojin Kasa (National Value Charter) ya tanada.

Karramawar da aka yi wa Mustapha Muhammad na zuwa ne a matsayin wani abin yabawa da ke nuna muhimmancin gaskiya da rikon amana a rayuwar yau da kullum, musamman ga wadanda ke rike da amanar jama’a.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version