Babban limamin masallacin Juma’a na Usman Bn Affan dake Unguwar Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale cikin birnin Kano Dr. Aliyu Muhammad Yunus, ya gargaɗi al’umma kan haɗarin alfahari da ayyukan alheri, yana mai cewa hakan na iya rage ko ma rusa ladan ayyukan da mutum ya yi.
Dr. Aliyu Yunus ya bayyana hakan ne a cikin hudubar da ya gabatar,ta yau Juma’a 19 ga Watan Zulhijja 1447 bayan Hijra inda ya jaddada muhimmancin yin ayyukan alheri domin neman yardar Allah kaɗai, ba don yabon mutane ko neman suna ba.
Ya ce daga cikin dabarun da shaidan ke amfani da su wajen ruɗar mutane akwai sanya su su riƙa ganin ayyukan alherin da suka yi a matsayin wani babban abin alfahari.
A cewarsa, bayan mutum ya yi aiki na gari, shaidan kan yi ƙoƙarin cusa masa girman kai da jin cewa ya fi wasu, lamarin da kan iya lalata ikhlasi da rage ladan aikin.
Malamin ya bayyana cewa abin da ya kamata mumini ya yi bayan kammala aikin alheri shi ne ya roƙi Allah Ya karɓi aikin nasa, domin babu wanda zai tabbatar da cewa an karɓi aikinsa sai Allah.
Ya ce maimakon alfahari da aikin da aka yi, ya kamata a riƙa jin tsoron kada wani kuskure ko gazawa ta hana karɓuwarsa.
Dr. Aliyu Yunus ya kawo misali da yadda Annabi Ibrahim da ɗansa Annabi Isma’il suka gina Ka’aba, duk da girman wannan aiki da darajarsa a wajen Allah, ba su yi alfahari da shi ba.
Maimakon haka, sun kasance suna addu’a suna cewa:
“Ya Ubangijinmu! Ka karɓa mana, lallai Kai ne Mai ji, Masani.”
Ya ce wannan aya tana nuna yadda annabawa, duk da girman ayyukansu, suka kasance suna neman Allah Ya karɓi ayyukansu, maimakon su yi girman kai ko su ga cewa sun kai wani matsayi na musamman.
Sannan ya bada misali da aikin Hajji da shima idan an kammala Allah ya neman Mahajjata su godewa Allah kuma su tuba.
Malamin ya tunatar da muminai cewa Allah Madaukakin Sarki ne kaɗai Ya san hakikanin ayyukan bayinsa da niyyoyinsu, don haka ya kamata kowa ya riƙa duba zuciyarsa tare da kiyaye ayyukansa daga riya, nuna kai da neman yabo daga mutane.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su yi taka-tsantsan da ruɗin shaidan, su ci gaba da gudanar da ayyukan alheri cikin tawali’u da tsoron Allah, tare da yawaita addu’ar neman karɓuwar ayyukansu.
Dr. Aliyu Yunus ya ce mumini na gaskiya shi ne wanda ke yin aikin alheri saboda Allah, sannan bayan ya kammala shi ya ci gaba da neman gafara da addu’ar Allah Ya karɓa masa, kamar yadda annabawan Allah suka koyar.
