Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Barau Jibiril ya amince da nadin Shehu Isah a matsayin babban mai taimaka masa kan harkokin majalisar.

A wata sanarwa da TST Hausa ta samu na nadin Direba ta gano cewa nadin ya fara aiki ne tun ranar 1 ga Afirilun, 2025.

A cikin takardar sanarwar wanda Sakataren Ma’aikata da ci gaban Jami’ai na Majalisar dattawa Essien Eyo Essien, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewar nadin na Shehu Isah ba na din din din ba ne fansho na dan lokaci, kamar yadda ake yi wa irin wannan mukami a tsarin gwamnatin tarayya.

Haka kuma, an bayyana cewa nadin Yana karkashin kulawar kare ra’ayin shugaban da yake aiki karkashinsa, wato Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ke da ikon soke ko tabbatar da nadin bisa ga tanadin aiki.

Majalisar dattawan taya shi murna bisa samun wannan muhimmiyar dama ta yi wa kasa hidima.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version