Wani rahoto daga hukumar kula da albarakatun man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ya nuna cewa ’yan Najeriya sun kashe kimanin Naira tiriliyan 1.58 wajen sayen man fetur a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ciko-a-tudu-an-shayen-giya-ta-sama-da-naira-tiriliyan-1-a-najeriya-cikin-wata-9/
A cewar rahoton, watan Disamba ya kasance lokaci na ƙaruwar tafiye-tafiye,da bukukuwa da harkokin kasuwanci, lamarin da ya sa akayi amfani da kimanin lita miliyan 63.7 na man fetur a kowace rana a fadin ƙasar nan.
Jimillar man fetur da akayi amfani da shi a cikin kwanaki 31 na watan ya kai kusan lita miliyan dubu 1 da miliyan dari 9 inda aka yi kiyasin kuɗaɗen bisa matsakaicin farashin kusan Naira 800 kan kowace lita.
Rahoton ya kuma nuna cewa a wasu sassan ƙasar, musamman Arewa, farashin fetur ya haura wannan adadi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/who-ta-yi-kira-da-a-kara-haraji-kan-barasa-da-abubuwan-sha-masu-dauke-da-sikari/
Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa wannan yawan kuɗi da aka kashe na nuna irin matsin da farashin man fetur ke dora wa rayuwar jama’a, musamman bayan cire tallafin man fetur, wanda ya bar farashi yana bin yanayin kasuwa, koda yake gwamnatin tarayya tace da yawa daga cikin yan Najeriya basa shayin kashe kudi duk da matsin da ake ciki.
Rahoton ya jaddada cewa idan ba a ɗauki matakan rage tsadar sufuri da inganta hanyoyin samar da makamashi ba, farashin fetur zai ci gaba da yin tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma da harkokin kasuwanci.
