Wata ƙungiya ta tsoffin Kwamishinoni a Jihar Kano zamanin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Gwamna daga Shekarar (2015–2023) ta bayyana cikakken goyon bayanta ga nadin Hon. Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano.
A cikin wata wasiƙa ta hadin guiwa da suka aike wa Gwamnan Jihar Kano a ranar 17 ga Afrilu, 2026, ƙungiyar ta bayyana cewa sun yi aiki tare da Murtala Garo a lokacin da suke rike da muƙaman gwamnati, inda suka shaida irin ƙwarewarsa, da jajircewarsa da ƙwazon sa wajen hidimtawa jama’a.
Sun bayyana shi a matsayin jagora mai ƙwarewar gudanarwa da siyasa, wanda zai ƙara wa gwamnatin Kano ƙarfi wajen aiwatar da manufofin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.
Ƙungiyar ta ce nadin Garo zai taimaka wajen ƙara inganta aikin gwamnati da kuma tabbatar da nasarar manufofin gwamnatin jihar.
Sunayen masu sa hannu sun haɗa da:
Hon. Muhammad Sanusi Kiru
Hon. Muhammad Garba
Hon. Muntari Ishaq Yakasai
Hon. Ibrahim Ahmed Karaye
Hon. Lamin Sani
Hon. Dr. Mariya M. Bunkure
Hon. Bappa Muhammad Takai
Hon. Barrister M. A. Lawan
Hon. Saleh Kausani
Hon. Idris Wada
Hon. Dr. Zahra’u Muhammad
Hon. Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa
Rt. Hon. Ya’u Abdullahi Yanshana
Hon. Garba Yusuf Abubakar
Hon. Mahmud Muhammad Santsi
Hon. Kabiru Ibrahim Getso
Hon. Ibrahim Dan’Azumi Gwarzo.
Ƙungiyar ta kuma aika kwafin wasiƙar zuwa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.
