Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da daukar matakan da suka dace wajen yaki da sauyin yanayi domin magance gurbacewar muhalli.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a aka rabawa manema labarai.

Shirin wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar, yana da manufar kare lafiyar jama’a, da rage hayaki mai gurbata muhalli da kuma samar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

A yayinda yake mika kundin Shirin ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf,kwamishinan Muhalli da sauyin yanayi Dokta Dahiru Muhammad Hashim,yace shirin zai maida hankali wajen inganta aikin noma, da makamashi, da Lafiya,da Sufuri,da Ilimi, da kuma haɓaka birane a Kano.

Dokta Hashim ya jaddada mahammcin mayar da hankali kan hanyoyin matsalolin sauyin yanayi na cikin gida, haɗin gwiwar kasashen duniya, ta hanyar samun tallafi daga kungiyoyin kasashen waje.

Gwamna Yusuf yace duka wannan na cikin manufofin gwamnatinsa na samar da Muhalli mai tsafta ga al’ummar Kano.

Yace acikin shirin akwai manufar farfado da tattalin arziki da bunkasar harkokin kasuwanci da zuba jari.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version