Gwamnatin Masarautar Saudiyya ta takaita wa’adin da masu rike da bizar Umrah za su iya shiga kasar daga watanni uku zuwa kwanaki 30 kacal, a wani sabon tsari da ya fara aiki daga ranar 1 ga Maris.
Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wanda aka fitar wa bizar Umrah dole ne ya shiga cikin Saudiyya cikin kwanaki 30 daga ranar da aka bayar da ita.
Idan aka wuce wannan wa’adi ba tare da an shiga kasar ba, to za’a soke ta kai tsaye.
Sai dai hukumomi sun jaddada cewa adadin kwanakin da mahajjaci zai yi bayan ya isa kasar bai sauya ba.
Wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren da mahukunta ke aiwatarwa domin kara inganta kula da cunkoso, da hana masu wuce wa’adin zama, da kuma daidaita kwararar alhazai yayin da shirye-shiryen Hajjin 2026 ke kara kankama.
Masana harkokin tafiye-tafiye sun bayyana cewa sabon tsarin na bukatar karin tsari da shiri daga masu niyyar Umrah da kuma kamfanonin yawon ibada, inda ake shawartar su tabbatar da kammala shirye-shiryen tafiya kafin neman biza domin gujewa yiwuwar soke ta sakamakon wuce wa’adin kwanaki 30.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hajj-2026-humumar-alhazan-kano-ta-sanar-da-ranar-fara-jigilan-maniyata-zuwa-saudiyya/
Ana sa ran cewa hukumomin Saudiyya za su ci gaba da daukar karin matakai yayin da ake kara kusantar zangon Hajjin 2026, domin tabbatar da tsari, tsaro da saukin gudanar da ibadar.
