A wani mataki da ya nuna gaskiya, riƙon amana da kishin tabbatar da adalci, Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Kano, Malam Mustapha Muhammad ya mayar da kuɗin Riyal 6,000 da aka yi masa kari bisa kuskure yayin rabon hakkokin yan Jarida da aka tanadarwa tawagar masu aikin yada labarai a Hajjin bana a ƙasa mai tsarki.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa Sakataren ƙarin kuɗin ne fiye da abin da ya dace ya karɓa.

Sai dai bayan ya gano kuskuren, bai yi wata-wata ba wajen mayar da kuɗin domin a daidaita lissafi tare da tabbatar da cewa an bai wa kowa haƙƙinsa yadda ya kamata.

Kudaden riyar 6,000 sun tasamma sama da naira miliyan biyu.

Mustapha Muhammad wanda shine jagoran tawagar yan Jarida da sukayi aikin yada labarai a kasa mai tsarki daga Kano yace mayar da kudaden ya zama wajibi domin samun damar biyan hakkin wasu.

Matakin da Mustapha ya ɗauka ya jawo yabon mutane da dama, musamman ma daga cikin abokan aikinsa da masu bibiyar harkokin gwamnati, da jagororin aikin hajjin bana a kasa mai tsarki waɗanda suka bayyana shi a matsayin abin koyi na gaskiya da riƙon amana a hidimar jama’a.

A yayinda yake karbar kudaden Mai martaba sarkin Gaya kuma Amirul Hajj na bana daga Kano Dr. Abubakar Abdulkadir Gaya ya bayyana matakin a matsayin adalci da gaskiya da nuna ya kamata.

Yace a lokacin da ake yawan kira ga jami’an gwamnati da masu riƙe da amanar jama’a su kasance masu gaskiya da adalci, irin wannan mataki yana ƙara tabbatar da cewa har yanzu akwai masu kishin gaskiya da ke fifita amana fiye da wata fa’ida ta kashin kai.

Ya kara da cewa dawo da kuɗin ya kara tabbatar da gaskiyarsa har ma ya taimaka wajen tabbatar da cewa wasu daga cikin masu aikin yaɗa labarai sun samu haƙƙoƙinsu ba tare da wani tangarda ba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version