Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya a Jihar Kano, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana matuƙar takaicinsa da jimami bisa sace Sakataren Mulki na ƙaramar hukumar Kibiya, Hon. Hamza Durba, da wasu ’yan bindiga suka aikata.

Ya bayyana cewa wannan lamari abin Allah wadai ne matuƙa, yana mai jaddada cewa hakan na ƙara nuna muhimmancin haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen irin waɗannan ayyukan ta’addanci da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

A wata sanarwa da mai magana da yawun dan majalisar Hon. Fatihu Yusuf Bichi ya fitar yace a halin yanzu, suna ci gaba da tattaunawa da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an kubutar da wanda aka sace cikin ƙoshin lafiya cikin gaggawa.

Haka kuma ya nuna ƙwarin gwiwa cewa jami’an tsaro za su ɗauki matakan da suka dace wajen gano waɗanda suka aikata wannan laifi tare da gurfanar da su a gaban doka.

Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai da bayanan da za su taimaka wajen samun nasarar wannan aiki.

Ya roƙi Allah da Ya kubutar da shi lafiya, tare da kare al’umma daga duk wani nau’in rashin tsaro.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version