Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa marigayin ya bar musu wasiyar cewa duk lokacin da ya rasu a binne gawarsa a birnin Madina.

Daya daga cikin iyalansa kuma yar uwa ga uwar gidan marigayin da ta rasu shekaru biyu da suka gabata Hajiya Amina Umar Fulani ce ta shaida hakan a zantawarta da TST Hausa a safiyar yau Asabar.

Tace marigayin ya bada wannan wasiyar ne tun bayan rasuwar matarsa marigayiya Hajiya Rabi Tajo Dantata a Madina.

Tun safiyar yau Asabar Shugaban majalisar Malamai ta Kano Shiek Ibrahim Khalil ya sanar da cewa za’ayi sallar Ga’ib ga mamacin Alhaji Aminu Dantata a masallacin Juma’a na Aliyu Bn Abi Dalib dake Dangi a birnin Kano da karfe 2 na rana.

Ya rasu a Dubai daga nan za’a dauki gawarsa zuwa birnin Madina domin binne gawarsa a kusa da uwar gidansa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version