Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da kashe jimillar kudi naira biliyan 61.63 domin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da suka shafi ilimi, ruwan sha da kiwon lafiya,da ababen more rayuwa,da noma da bunƙasa birane.
An amince da hakan ne bayan kammala zaman majalisar karo na 39 da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Kano.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana wa manema labarai cewa matakin na nuna ƙudirin gwamnati na inganta ayyukan jama’a da kuma hanzarta ci gaban tattalin arziki a faɗin jihar.
Kwamared Waiya ya ce an ɗauki matakan ne bayan nazari mai zurfi kan muhimman bukatun al’umma, tare da mai da hankali kan kyautata rayuwa da faɗaɗa samun ayyukan yau da kullum.
Ilimi Na Kan Gaba
A fannin ilimi, an ware sama da naira biliyan 4.45 domin biyan kuɗin jarabawar waje ga ɗaliban da za su rubuta jarabawar NECO da NABTEB da NBAIS a shekarar 2026.
Haka kuma, majalisar ta amince da naira biliyan 2 domin samar da kujeru da tebura ga makarantu a ƙananan hukumomi 30, tare da gina da gyaran ajujuwa a Makoda, Tarauni, Ajingi da Minjibir.
An kuma amince da biyan basussukan kuɗaɗen jarabawa daga 2020 zuwa 2023, da kuma kuɗin ciyar da ɗaliban makarantu masu kwana.
Ƙarfafa Sashen Lafiya
A bangaren lafiya, an amince da gyaran Babban Asibitin Wudil tare da samar da kayan aiki na zamani ga asibitoci.
Haka kuma, an ware kuɗaɗe domin shirye-shiryen rigakafi, yaƙi da cutar shan inna a dukkan ƙananan hukumomi 44, da kuma samar da kiwon lafiya kyauta ga mata masu juna biyu, jarirai da ƙananan yara a cibiyoyi 484.
Gina Ababen More Rayuwa
A fannin ababen more rayuwa, an amince da sama da naira biliyan 5.2 domin gina hanyar Panshekara Underpass zuwa gadar Madobi, tare da gyaran hanyoyi a ƙaramar hukumar Gwale.
Sauran ayyuka sun haɗa da gyaran ofisoshin gwamnati, da inganta sansanin horas da matasa na NYSC a Kusalla, da kuma wasu gine-ginen gwamnati.
Noma, da samar da Ruwa da inganta Muhalli.
Domin bunƙasa noma, an amince da kusan naira biliyan 3.5 domin sayen takin zamani sama da buhu 41,000, tare da ƙarfafa harkokin ban ruwa.
A bangaren ruwa, an ware naira biliyan 3.48 domin gyaran matatar ruwan Tamburawa da kuma samar da rijiyoyin burtsatse.
Haka kuma, an amince da ayyukan gyaran muhalli kamar kawata birane da gyaran magudanan ruwa.
Bunƙasa Birane da Sauran Shirye-shirye
Majalisar ta kuma amince da ayyukan bunƙasa birane, ciki har da biyan diyya, gina hanyoyi da kuma kafa Kwalejin Fasaha ta Gaya.
Sauran abubuwan sun hada :
Ayyukan tallafi a ƙananan hukumomi 15.
Biyan haƙƙoƙin ma’aikata a Jami’ar Aliko Dangote da sayen kayan ICT domin inganta sadarwar gwamnati tallafa wa sana’o’i da shirye-shiryen aikin Hajji Gwamnati Ta Jaddada Aniya Ibrahim Abdullahi Waiya ya tabbatar da cewa za a aiwatar da dukkan ayyukan cikin gaskiya da bin ƙa’ida, yana mai cewa gwamnati na da burin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da kuma isar da ribar dimokuraɗiyya ga al’umma.
