Limamin Masallacin Annabi Muhammadu SAW a birnin Madina a kasar Saudiyya Sheikh Hussain bin Abdulaziz Al Sheikha yi kira ga al’ummar Musulmi da su ƙara tsoron Allah tare da amfani da falalar watan Ramadan Musmaman goman karshe wajen ƙara ibada da aikata ayyukan alheri.
TST Hausa ta rawaito cewa limamin ya tunasar da masu azumi da su kara kusantar Allah sannan suji tsoransa, ya na mai cewa kwanaki 10 na karshen Ramada watakila ya zamo sune kwanaki karshe ga wasu ba tare da riskar irin wannan damar a wata shekarar ba.
Sheikh Hussain ya bayyana hakan ne yayin hudubar sallar Juma’a ta yau 17 ga watan Ramadan 1447 bayan hijira inda ya tunatar da dubban masu ibada da suka halarci sallar kan muhimmancin tsoron Allah (taqwa) a rayuwar Musulmi.
A cikin hudubar tasa, limamin ya jaddada cewa tsoron Allah shi ne ginshiƙin rayuwar mumini, domin yana taimaka wa mutum ya nisanci sabo tare da ƙara himma wajen aikata ayyukan alheri da za su kusantar da shi ga Ubangiji.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/hudubamatasan-yanzu-idon-su-ya-rufe-da-neman-kudi-shiyasa-suke-saka-kansu-a-caca-da-crypto-dr-abdullah-gadon-kaya/
Ya kuma bayyana cewa watan Ramadan wata babbar dama ce da Allah Ya bai wa bayinsa domin su ƙara kusantarsa, ta hanyar yawaita karatun Al-Qur’ani, da yin addu’o’i, da bayar da sadaka, da kuma tsayuwar dare wajen ibada.
Haka zalika, Sheikh din ya gargadi masu azumi da su guji halaye marasa kyau kamar ƙarya,da zagi, da cutar da mutane, yana mai cewa irin waɗannan halaye na rage daraja da ladan azumi.
limamin ya buƙaci Musulmi su ƙara kyautata mu’amala da juna tare da taimakon marasa ƙarfi da masu buƙata, domin samun rahama da falalar Allah a cikin wannan wata mai albarka na Ramadan.
Sannan yayi adu’a ta Musmaman kan halin da kashashen musulmi ke ciki Musmaman a gabas ta tsakkiya, domin samun zaman lafiya.
