Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi fatali da bukatar da Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja, ya gabatar na neman izinin fita zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Akanta Janar din na fuskantar tuhuma kan zargin hannu a badakalar karkatar da kudaden gwamnati da suka haura naira miliyan dubu 1 da miliyan 600, zargin da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ke yi masa tare da wasu mutane.
Yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayyana cewa kotun ba ta gamsu da dalilan da aka gabatar wajen neman wannan izini ba, musamman duba da yadda shari’ar ke gaban kotu kuma ake ci gaba da sauraren ta.
Kotun ta ce ba za ta bayar da damar da ka iya kawo tsaiko ko tangarda ga shari’ar ba, sannan ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2026.
Lauyoyin masu gabatar da kara sun yi maraba da matakin kotun, yayin da ake sa ran bangarorin shari’ar za su sake bayyana a gaban kotun a ranar da aka sanya domin ci gaba da shari’ar.
