Jigo a Jam’iyyar PRP kuma mai neman takarar majalisar tarayya a zaben 2027 daga Dala a PRP Hon. Ali Rabiu Ali, ya bayyana cewa har yanzu ƙofar jam’iyyar a buɗe take domin karɓar jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, idan ya yanke shawarar komawa cikinta.
Ali Rabiu Ali ya yi wannan bayani ne a yayin tsokaci kan sauye-sauyen da ke gudana a fagen siyasar ƙasar nan ta cikin wani sakon murya da ya aikewa TST Hausa , inda ya nuna shakku kan yiwuwar samun mafita ta siyasa a sabuwar NDC da Kwankwaso ya koma.
A cewarsa, duk da cewa sauya jam’iyya hakki ne na ɗan siyasa, amma yana da muhimmanci a zaɓi dandalin da ya dace da akida da manufofin mutum kamar PRP wacce aka samar da ita saboda talaka.
Ya jaddada cewa PRP na da tushe mai ƙarfi,da tarihi, da kuma tsayayyun manufofi da suka yi daidai da irin salon siyasar Kwankwaso.
Ya kuma ƙara da cewa dawowar Kwankwaso PRP na iya ƙara ƙarfafa jam’iyyar da kuma samar da sabuwar hanya ga magoya bayansa a fagen siyasa kuma kamar ya dawo gida ne.
Hon. Ali Rabiu yace duk sauran jamiyyun siyasa babu wacce ta dace da talaka kamar PRP.
Sai dai zuwa yanzu, Rabiu Musa Kwankwaso bai fito fili ya bayyana mataki na gaba da zai ɗauka ba dangane da makomarsa ta siyasa, lamarin da ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu ruwa da tsaki.
