Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, zai halarci Sallar Juma’a ta musamman da za a gudanar ranar 25 ga Satumba, a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cikar ƙasar shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Za a gudanar da sallar ne domin tunawa da ranar da Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka a shekarar 1960, tare da yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasar.
Sallar Juma’ar za ta kasance cikin jerin shirye-shiryen bikin ’yancin kan na bana, wanda Gwamnatin Tarayya ta ce za a gudanar cikin sauƙi.
Shirin zai fara da taron manema labarai na duniya ranar 24 ga Satumba, sannan Sallar Juma’a ta musamman ranar 25 ga Satumba, da ibadar coci ranar 27 ga Satumba.
Haka kuma, an tsara gudanar da lacca ta musamman kan ranar ’yancin kai ranar 30 ga Satumba, kafin Shugaba Tinubu ya gabatar da jawabin ƙasa baki ɗaya ga ’yan Najeriya ranar 1 ga Oktoba, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.
