Majalisar Sasanta Matsalolin Ma’aikata da Gwamnati ta Kasa (JNC) reshen Jihar Kano ta yabawa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa tallafin Naira dubu 20 da ya bai wa kananan ma’aikatan jihar domin rage musu radadin matsin tattalin arziki a yayin bukukuwan Babbar Sallah ta bana.
Majalisar ta bayyana tallafin a matsayin wani mataki na jin kai da kulawa, wanda ya taimaka matuka wajen saukaka wa ma’aikata nauyin kashe-kashen da ke tattare da bukukuwan Sallah, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen tattalin arziki.
A cikin wata sanarwa da Shugaban JNC na Jihar Kano, Kwamared Hashim A. Saleh, ya fitar, ya ce matakin da gwamnan ya dauka ya nuna irin damuwarsa da walwala da jin dadin ma’aikatan gwamnati a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa tallafin da aka bai wa ma’aikatan da ke matakan albashi na daya zuwa goma sha hudu ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na inganta rayuwar ma’aikata da kuma tallafa musu a lokutan da suke bukatar hakan.
JNC ta kuma yabawa Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, da Shugaban Ma’aikatan Jiha, da sauran jami’an gwamnati bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago a jihar.
A sanarwar mai dauke da sa hannun Jami’in Hulda da Jama’a na JNC na Jihar Kano, Kwamared Haladu Musa, majalisar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da hada kai da gwamnatin jihar wajen tabbatar da zaman lafiya a wuraren aiki da kuma kara inganta ayyukan yi domin amfanin al’umma.
Majalisar ta kuma yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su nuna godiyarsu ga wannan karamci ta hanyar kara himma, rikon amana, biyayya ga dokokin aiki da kuma sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu domin ci gaban Jihar Kano.
