Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Kano ta ɗauki tsauraran matakan ladabtarwa kan wasu alkalan kotunan shari’a da ma’aikatan kotu bayan samun su da laifukan cin hanci, nuna son kai da kuma karya dokokin aiki.
Matakin ya biyo bayan taron Hukumar karo na 89 da aka gudanar a ranar 16 ga Afrilu, 2026, inda aka amince da rahotannin bincike na Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Harkokin Shari’a (JPCC).
Manyan Matakan da aka dauka sun hada da janye wasu alkalan kotu daga aikin shari’a.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kotunan Kano Baba Jibo Ibrahim ya fitar yace an rage wa wasu ma’aikata matsayi sannan wasu kuma an bayar da gargaɗi mai tsanani ga wasu.
Baba Jibo yace hukumar ta bai wa Mahmud Ahmad, jami’in sufuri a Babbar Kotun Jihar Kano, gargaɗi mai tsanani bayan an same shi da yin amfani da sunan Hukumar wajen tsoratar da jama’a da kuma wuce iyakar aikinsa.
A bangaren shari’a, an ladabtar da Mallam Salisu Buhari Mandawari, Alkalin Kotun Shari’a ta Rogo, bisa samunsa da laifukan karɓar cin hanci da rashin gudanar da rubutun shari’a yadda ya kamata.
Hukumar ta rage masa matsayi da matakai biyu tare da dakatar da shi daga aikin shari’a na tsawon shekaru uku, tare da rabin albashi.
Haka kuma, an janye Alkali Umar Sunusi Danbaba (Ph.D) daga aikin shari’a na tsawon shekaru uku bayan an same shi da nuna son kai, rashin kula da kuɗaɗe da kuma wasu halaye da suka saɓa wa ƙa’idojin aiki.
Za a biya shi rabin albashi na tsawon shekara guda.
A Kotun Shari’a ta Rogo, bincike ya nuna cewa Abdulbari Ado da Umar Abdulhamid,magatakardar kotu, sun shiga harkar neman da karɓar cin hanci.
Hukumar ta rage musu matsayi da matakai biyu tare da rabin albashi na shekara guda, tare da gargaɗi mai tsanani.
A wani lamari dabam, an cire Sabiu Adam Inusa, rajistan kuɗi na Kotun Shari’a ta Gwarzo, daga mukaminsa bayan bayar da rasiti mai saɓani.
Duk da cewa an ɗauki kuskuren a matsayin na rashin niyya, Hukumar ta ɗauki matakin ne domin kiyaye sahihancin aikin kotu.
Sanarwar tace hukumar ta kuma amince da naɗin Hussaini Hassan Suleiman a matsayin Babban Rajista na dindindin na Babbar Kotun Jihar Kano.
Hukumar ta jaddada aniyarta na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da bin doka a harkokin shari’a, tana mai gargadin cewa ba za a lamunci duk wani nau’i na rashin ɗa’a ba.
