Daya daga cikin limaman Masallacin Harami a Makka Sheikh Maher Al-Muaiqly wanda ya jagoranci sallar Juma’a ya bukaci Musulmi da su yi amfani da falalar kwanaki goma na farkon watan Dhul-Hijjah wajen kara kusanci ga Allah ta hanyar ibada da ayyukan alheri.

A hudubar Juma’ar da ya gabatar Sheikh Maher Al-Muaiqly ya bayyana cewa kwanakin farko na Dhul-Hijjah na daga cikin mafiya daraja a Musulunci, saboda irin falalar da Allah Ya tanadar a cikinsu.

Ya bukaci Musulmi su yawaita zikiri, istigfari, karatun Alkur’ani, sadaqa da sauran ayyukan alheri domin samun lada mai yawa.

Limamin ya kuma yi bayani kan muhimmancin ranar Arfa, yana mai cewa rana ce ta rahama, gafara da kubutar da bayin Allah daga azabar wuta. Ya karfafa wa wadanda ba sa aikin Hajji gwiwar yin azumin ranar Arfa saboda falalar da ke tattare da ita.

TST Hausa ta rawaito cewa hudubar ta mintuna 15 saboda tsananin zafin rana Sheikh Maher Al-Muaiqly ya tunatar da alhazai muhimmancin tsarkake niyya, bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), da kuma kiyaye hadin kai da zaman lafiya tsakanin Musulmi.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version