Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kama wasu matasa biyu mace da Namiji da suka daura aurensu a gidan cin abinci da shakatawa na Banana dake unguwar Zoo road a cikin birnin Kano.

Mataimakin kwamandan Hisba na Jihar Kano a bangaren kai simame da ayyukan yau da kullum Dr Mujahideen Amenuddeen shine ya shaida hakan ga manema labarai a birnin Kano.

Yace bayan samun labarin daura auren ma’auratan guda biyu a gidan cin abinci ba tare da waliyansu ba ,sai suka dana tarko domin kamasu ,saboda suna yawan zuwa wajen shakatawa bayan daura auren nasu.

Dr Mujahideen ya shaidawa Jaridar TST Hausa cewa sun kama ma’auratan ne a cikin daren ranar Laraba lokacin da sukaje wajen shakatawa.

Mataimakin kwamandan Hisbar yace abinda sukayi ya Saba da shari’a kuma abin takaici ne ,ace an daura auren mutanan biyu babu ko daya daga wakilcin iyaye ko yan uwa saidai wakilcin abokai kawai wadanda ma duka kazo nazo ne.

A yanzu haka matasan mace da namijin suna hannun Hisba domin gudanar da bincike.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version