Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa ta karɓi bizar dukkan maniyyatan jihar da suka yi rijista domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026, kuma an riga an buga su tare da liƙa su a cikin fasfofinsu na ƙasa da ƙasa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Suleiman A Dederi ya fitar yace Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana daga Ƙasar Saudiyya, inda ya tabbatar wa al’umma cewa babu wata matsala ko jinkiri da hukumar ke fuskanta dangane da batun fitar da bizar alhazan Jihar Kano.

Ya ce dukkan maniyyatan da suka kammala rajista sun riga sun samu bizar su, don haka babu wani dalili na damuwa ga iyalai da alhazan da ke shirin gudanar da ibadar Hajji a bana.

Alhaji Matawalle ya kuma yi kira ga maniyyatan Hajji da sauran jama’a da su yi watsi da duk wata jita-jita ko bayanai marasa tushe da ke yawo a kafafen sada zumunta, musamman waɗanda ke cewa akwai jinkiri ko matsala wajen fitar da bizar alhazan jihar.

Ya buƙace su da su guji yaɗa ko amincewa da hanyoyin yanar gizo, saƙonni ko rahotannin ƙarya da ka iya jawo ruɗani a tsakanin jama’a.

Babban Daraktan ya ƙara da cewa jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano na ci gaba da aiki a Ƙasar Saudiyya, inda suke gudanar da muhimman shirye-shirye domin tabbatar da cewa an kammala dukkan tsare-tsare da suka dace, ta yadda alhazan jihar za su gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi, tsari da kwanciyar hankali.

Hukumar ta kuma tabbatar wa dukkan maniyyatan da suka yi rijista cewa ana ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da jin daɗinsu, tsaronsu da kuma ingantaccen kulawa da harkokinsu a duk tsawon lokacin gudanar da aikin Hajji.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version