Hukumar kula da Jin daɗin Alhazzan Jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da binciken lafiya da yin allurar rigakafi ga dukkan maniyyatan da ke shirin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026.

Darakta Janar na hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake duba ayyukan cibiyar horar da maniyyata da ke Karamar Hukumar Gwarzo.

Ya ce za a fara gudanar da aikin ne daga ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairu, 2026, kuma za a gudanar da shi a Asibitin sansanin maniyyata (Hajj Camp), Kano.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a Kwamared Sulaiman Dederi yace darakta Janar ɗin, wanda Daraktan Ilmantarwa da Wayar da Kai, Alhaji Murtala Lawan Sani, ya wakilta, ya jaddada cewa bin ƙa’idoji da dokokin Hukumar yadda ya dace zai taimaka wajen tabbatar da tafiyar aikin Hajji cikin sauƙi,da tsari da nasara.

KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-ya-baiwa-mutumin-da-aka-kashewa-ya-ya-6-da-mata-kujerar-aikin-hajji-da-umara/

Ya ƙara da cewa aikin zai haɗa da cikakken binciken lafiya, yin allurar rigakafi, da kuma gwajin ciki ga maniyyata mata, kamar yadda ƙa’idojin lafiyar aikin Hajji na ƙasa da ƙasa suka tanada.

Da yake jawabi kan Darasin Shirye-shiryen Hajji, Darakta Janar ya shawarci maniyyata da su kasance masu kulawa da darussa, tare da bin koyarwar malamansu domin su fahimci yadda ake gudanar da ibada yadda ya kamata a Ƙasar Harami.

Haka kuma, ya yi kira ga maniyyata da su bi jadawalin tafiye-tafiyensu ba tare da tangarda ba, tare da kasancewa a cikin rukunonin Kananan Hukumomin da aka ware musu domin kauce wa ruɗani.

A yayin zagayen sa ido, tawagar Hukumar ta kai ziyara Kananan Hukumomin Gwarzo da Rimin Gado, domin duba yadda shirye-shiryen aikin Hajjin ke tafiya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version