Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa za a fara jigilar maniyyatan Hajjin shekarar 2026 zuwa ƙasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu.
Sanarwar ta fito ne daga babban daraktan hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle, yayin bikin rufe taron horas da maniyyata da aka gudanar a Makarantar Nazarin harshen Larabci da ke Kano, a wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
Ya bayyana cewa jadawalin jigilar ya biyo bayan tsarin da hukumar Alhazai ta Najeriya ta fitar, inda aka tanadi ranar 14 ga Mayu a matsayin ranar tashin jirgi na farko daga Kano, tare da kamfanin Max Air a matsayin wanda zai gudanar da jigilar.
Matawalle ya jaddada cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace tun kafin lokaci, domin tabbatar da fara aikin Hajjin cikin tsari, sauƙi da nasara.
A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar, Yusuf Lawan, ya shawarci maniyyata da su ci gaba da nazarin littattafan horaswa da aka basu, yana mai cewa hakan zai taimaka musu wajen gudanar da ibadar Hajji cikin fahimta da nutsuwa.
Haka kuma ya buƙace su da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin da hukumomin Najeriya da na Saudiyya suka gindaya, domin kauce wa duk wata tangarda yayin aikin Hajjin.
A taron, jami’an tsaro da hukumomi masu ruwa da tsaki a harkar Hajji—ciki har da Hukumar Shige da Fice, NDLEA, Kotun Hajji, NOA, da Hisbah tare da kamfanin Max Air—sun gabatar da muhimman shawarwari da gargadi ga maniyyatan.
