Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar bazata zuwa Asibitin Kwararru na Best Choice da ke Tal’udu Junction a Kano, domin duba yadda ake gudanar da ayyukan kula da lafiyar al’umma, musamman a lokutan dare tare nuna mamakinsa kan abinda ya tarar na kwarewar ma’aikata da kayan aikin dake Asibitin.

Gwamnan ya kai ziyarar ne a daren Juma’a, inda ya zagaya sassa daban-daban na asibitin tare da rakiyar likitan da ke bakin aiki da sauran ma’aikatan asibitin, domin tantance yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya.

A yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya duba marasa lafiya tare da tattaunawa da ma’aikatan asibitin kan yadda suke gudanar da ayyukansu.

Ya kuma yaba da yadda ya tarar da ma’aikatan cikin dare suna gudanar da ayyukan ceton rayuka kamar yadda ake yi da rana.

Gwamnan ya bayyana cewa kulawarsa ga harkar lafiya ba ta takaita ga asibitocin gwamnati kadai ba, domin yana kuma ba da muhimmanci ga cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu da ke taimakawa wajen samar da ingantacciyar kulawar lafiya ga al’ummar jihar Kano.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gode wa shugabannin Asibitin Best Choice da ma’aikatansa bisa jajircewarsu da sadaukarwarsu wajen kula da marasa lafiya, inda ya ba ma’aikatan wata kyauta ta musamman domin kara musu kwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Asibitin Best Choice Specialist Hospital da ke Tal’udu Junction, kusa da makarantar Sheikh Al-Rayyan a Kano, na gudanar da ayyukan kiwon lafiya na sa’o’i 24 a kowace rana, kwana bakwai a mako, tare da kwararrun likitoci da sauran ma’aikatan lafiya a sassa daban-daban.

Ziyarar ta sake nuna aniyar gwamnatin jihar na karfafa harkar lafiya da kuma tallafa wa dukkan cibiyoyin da ke taka rawa wajen kare rayuka da inganta lafiyar al’ummar Kano.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version