Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rabawa matasa 1,116 masu gudanar da sana’o’i a kan titunan cikin birnin Kano, ciki har da masu talla da masu faci, tallafin jarin Naira dubu 50,000 kowannensu, wanda jimillar kudinsa ta kai Naira miliyan 55.8, domin bunkasa harkokinsu.
Da yake jawabi yayin rabon tallafin a fadar gwamnatin Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin alkawurran da ya daukar wa matasa tun lokacin yakin neman zabensa, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da cika alkawurran da ta dauka.
Gwamnan ya ce yana jin kunyar irin dimbin kauna da goyon bayan da matasan Kano ke nuna masa, saboda haka yana ganin wajibi ne ya mayar musu da wannan kauna ta hanyar samar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta gajiya ba wajen ci gaba da tallafawa matasa, domin samar musu da damar dogaro da kai, rage zaman banza da kuma karfafa tattalin arzikin jihar.
A karkashin wannan shiri, matasa 1,116 sun amfana da tallafin Naira dubu 50,000 kowannensu, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 55.8, domin fadada sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
Yace yana sane da dukkanin wuraren da matasan ke sana’ar tallace tallace a kan titunan Kano.
Yace matasan abin a ja a jika ne saboda suka rungumi sana’arsu.
