Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya cika alkawarinsa na baiwa kowane Alhajin jihar kyautar kudi har Riyal 200 a matsayin barka da Sallah.
TST Hausa ta rawaito cewa an fara rabon kudaden ne a daya daga cikin masaukan Alhazan Kano da ke birnin Makka na Kasar Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar ta ware sama da naira miliyan 266 domin aiwatar da wannan shiri, wanda ya anfani Alhazan Kano sama da 3,600 da suka halarci aikin Hajjin bana.
Amirul Hajj na Jihar Kano, kuma Mai Martaba Sarkin Gaya, Dr. Aliyu Abubakar Abdulkadir Gaya, ne ya jagoranci rabon kyautar tare da wasu jami’an gwamnatin jihar da ke kula da harkokin Alhazai a kasa mai tsarki.
Da yake jawabi yayin rabon kudaden, Amirul Hajj ya bayyana cewa kyautar na daga cikin kokarin gwamnatin Kano na tallafawa Alhazanta tare da sanya musu farin ciki a yayin gudanar da ibadar Hajji da bukukuwan Sallah.
Wasu daga cikin Alhazan da suka amfana da kyautar sun bayyana jin dadinsu da wannan karamci na gwamnatin jihar, inda suka yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cika alkawarin da ya dauka tare da nuna kulawa ga Alhazan Kano.
Alhazan sun kuma yi addu’ar Allah Ya karbi ibadunsu, Ya saka wa gwamnatin jihar da alheri, tare da ci gaba da ba ta ikon gudanar da ayyukan da za su amfani al’ummar Kano.
