Babban Manajan Vision FM 92.5 Kano da Farin Wata TV Kano, Malam Anas Idris Hassan, ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma bikin Eid-el-Fitr, tare da fatan zaman lafiya,da haɗin kai da ci gaba ga kowa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Malam Anas ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa bai wa al’umma damar kammala wannan ibada lafiya, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da riko da darussan da watan Ramadan ya koyar musamman tausayi, haƙuri, sadaukarwa da tsoron Allah.

Ya kuma yabawa Shugaban Kamfanin Vision Media Services, Alhaji Umar Faruk Musa, bisa jajircewarsa da goyon bayansa wajen bunƙasa aikin jarida mai inganci a Najeriya.

KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/anas-idiris-hassan/

Sanarwar ta kuma isar da gaisuwa da godiya ga shugabannin sassa daban-daban,da abokan hulɗa, da kwastomomi, da dimbin masu sauraro da masu kallo a faɗin Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa:

“Muna gode wa Allah da Ya ba mu ikon kammala azumi lafiya. Wannan lokaci ne na godiya da kuma tabbatar da cewa mun ci gaba da rayuwa bisa kyawawan dabi’u da muka koya a watan Ramadan.”

Hakazalika, ya yi addu’a ta musamman ga Jihar Kano da ƙasar Najeriya baki ɗaya, yana roƙon Allah Ya tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.

A ƙarshe, Malam Anas ya roƙi Allah da Ya bai wa shugabanni a kowane mataki hikima, adalci da riƙon amana wajen jagorantar al’umma.

Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya kuma maimaita mana irin wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya da yalwar arziki.

Daga nan yayi fatan masu kafafen yada labarai a Arewa za suyi amfani da damar su wajen magance matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version