Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da sadarwa ga jama’a, Sunday Dare, ya mayar wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, martani kan yadda ya kira Shugaban Ƙasar da sunansa na farko, “Bola”.
Sunday Dare ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, yayin da yake martani kan kalaman Atiku a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Juma’a.
A yayin taron, Atiku Abubakar ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya amince da shawararsa ta sa baki domin rage farashin man fetur, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne a rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar man fetur.
Atiku ya ce idan gwamnati ta amince da shawarar, Shugaban Ƙasa zai iya sauya mata suna ko kuma ya ɗauki yabo, muddin hakan zai taimaka wajen rage farashin man fetur.
Sai dai a martaninsa, Sunday Dare ya ce kiran Shugaban Ƙasa da sunansa na farko tare da ba shi umarni kan yadda zai tafiyar da gwamnati bai dace da mutuncin ofishin Shugaban Ƙasa ba.
Dare ya kuma kare manufofin tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa gwamnatin na aiwatar da sauye-sauye da nufin sake fasalin tattalin arziƙin ƙasar.
Ya kuma yi suka kan shawarar Atiku ta rage farashin man fetur ta hanyar sa hannun gwamnati, yana mai cewa akwai buƙatar a duba tasirin irin wannan mataki ga tattalin arziƙin ƙasa.
Kalaman Sunday Dare sun zo ne kwana guda bayan Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya kuma soki Atiku kan kiran Shugaban Ƙasa da “Bola”.
Keyamo ya ce kiran Shugaban Ƙasa da sunansa na farko bai dace ba, yana mai cewa ya kamata a mutunta martabar ofishin Shugaban Ƙasa duk da bambancin ra’ayin siyasa.
A halin yanzu, Atiku Abubakar na cikin ’yan siyasar da ke bayyana ra’ayoyinsu kan yadda ya kamata a tafiyar da ƙasar gabanin zaɓen shekarar 2027, yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke shirin neman wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
