Kungiyar Malaman jami’oi ta Najeriya tayi watsi da kudurin dokar haraji ta 2024 da ke gaban majalisar dattawa domin amincewa da ita.

Shugaban Kungiyar Malaman jami’oi na Najeriya shiyar Kano Kwamared Abdulkadir Muhammad ya bayyana hakan a taron manema labarai da Kungiyar ta kira a ofishinta dake Kano.

Kungiyar ta ASUU shiyar Kano ta hada da jami’oin Ahamadu Bello dake Zaria da jami’ar Bayaro dake Kano data Aliko Dangote dake Wudil da jami’ar Northwest dake birnin Kano da jami’ar gwamnati tarayya dake Dutsen Jigawa da jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa da Kuma jami’ar Jihar Kaduna.

Kwamared Abdulkadir Muhammad yace a cikin dokar haraji ta 2024 sun gano ana neman janye tallafin kudaden da ake baiwa jami’oin Najeriya ta karkashin asusun tallafawa jami’oi na kasa TETFund.

Yace abinda suka gano idan har wannan doka ta tabbata ana so a rage abinda ake baiwa jami’oin Najeriya kaso 50 cikin 100 daga shekarar 2025 zuwa 2026.

Sannan Kuma daga shekarar 2027 zuwa 2028 da 2029 mutukar aka amince da dokar harajin ,to asusun tallafawa jami’oin Najeriya zai rika karbar tallafin kudaden ne kaso 66 cikin 100.

Kungiyar ta ASUU tace daga shekarar 2030 Kuma za’a daina bada ko naira daya zuwa asusun na TETFund.

Kwamared Abdulkadir Muhammad yace abinda suke tsoro idan aka tabbatar da wannan doka ta haraji shine sake jefa daliban Najeriya cikin mawuyacin hali a cikin jami’oin Najeriya.

Ya kara dacewa ta cikin wannan asusu na TETFund ne ake samun kudaden tallafin gine gine a cikin jami’oi da samar da kayan koyo da koyarwa da kuma bada horo na musamman ga dalibai da Malamai da tarukan karawa juna sani da sauransu.

TST Hausa ta gano cewa a shekarar 1992 bayan matsalolin da kungiyoyar ASUU ke fuskanta a zamanin mulkin Janaral Ibrahim Badamasi Babangida aka kirkiro asusun tallafawa Ilimi na ETF daga baya aka maida asusun na bai daya wato TETFund a shekarar 2011.

Kwamared Abdulkadir Muhammad ya tabbatar dacewa, muddin aka amince da wannan doka ta haraji ta 2024 daga majalisar dattawa ta kasa ,to kuwa da yawa daga cikin jami’oin Najeriya zasu rushe ko su kasa tafiyar da hakokinnsu na yau da kullum.

A ciki dokar idan har ta tabbata, za’a sauya asusun na TETFund da gwamnatin tarayya take zuba kudade a matsayin tallalfi zuwa sabon asusun bada lamuni ko rance ga jami’oi na TETFUND.

A dan haka ASUU reshen Kano ta nemi majalisar tarayya ta kasa da majalisar tattalin ARZIKI su gaggauta janye wannan dokar haraji daga gaban majalisar dattawa domin samawa yan Najeriya makoma mai kyau.

Abin jira a gani shine ko majalisar dattawa ko fadar Shugaban kasa zasu duba koken Malaman jami’oin kafin a kammala karatu na uku akan dokar ta haraji.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version