Shugaban rukunin Kamfanonin Alhaji Aliko Dangote, ya ce darajar hannayen jarin Matatar Man Dangote da ake sayarwa a yanzu kan naira 525 na iya tashi zuwa naira 10,000 a nan gaba.
Dangote ya kuma ce ƙananan masu zuba jari za su samu fifiko wajen rabon hannayen jarin da ake shirin fitarwa ga jama’a ta hanyar IPO.
Aliko Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi cikin harshen Hausa, inda ya yi bayani kan shirin fitar da hannayen jarin matatar da kuma irin damar da hakan zai samar wa masu zuba jari.
Dangote ya ce idan aka fara rabon hannayen jarin, ƙananan masu zuba jari da ke son sayen hannayen jari da darajarsu ta kai naira dubu 50 ko naira dubu 100 da makamantansu za su samu fifiko kafin manyan kamfanoni da masu zuba jari na hukumomi.
Ya ce manyan masu zuba jari da ke neman hannayen jari masu yawa ba za su samu duk abin da suka nema ba, saboda za a fara bai wa ƙananan masu zuba jari dama.
Ya ce bayan an ware wa ƙananan masu zuba jari abin da ya kamata, za a raba sauran hannayen jarin ga sauran masu neman saye.
Dangote ya kuma bayyana hasashensa cewa farashin hannayen jarin da ake sayarwa a kan naira 525 a yanzu na iya ƙaruwa sosai a nan gaba, har ya kai naira 10,000.
Ya bayar da misali da cewa idan mutum ya sayi hannayen jari da naira miliyan biyar a yanzu, idan farashin ya kai naira 10,000 a nan gaba, darajar jarinsa na iya wuce naira miliyan 50.
Sai dai wannan hasashe na Aliko Dangote ba ya nufin cewa lallai hannayen jarin za su kai wannan farashi, domin bayan fara cinikinsu a kasuwar hada-hadar hannayen jari, farashinsu zai iya tashi ko kuma ya ragu bisa la’akari da yanayin kasuwa da kuma yadda kamfanin ke gudanar da ayyukansa.
Dangote ya kuma ce masu hannayen jarin za su iya zabar karɓar rabon ribarsu, wato dividend, ko dai a naira ko kuma a dalar Amurka.
Ya ce wannan damar na iya taimaka wa masu zuba jari wajen rage tasirin faduwar darajar naira, musamman ga mutanen da ke da wasu nauyin biyan kuɗaɗe a ƙasashen waje.
Ya kawo misalin iyayen da ke da ’ya’ya da ke karatu a ƙasar Birtaniya, inda ya ce karɓar dividend a dalar Amurka na iya taimaka musu wajen fuskantar sauyin canjin kuɗi.
A halin yanzu, shirin IPO na Matatar Man Dangote ya ƙunshi hannayen jari biliyan 4.1, inda ake sayar da kowanne a kan naira 525.
Idan aka sayar da dukkan hannayen jarin, ana sa ran za a tara kusan naira tiriliyan 2.15.
Mafi ƙarancin adadin hannayen jari da mutum zai iya nema shi ne guda 10, wanda kudinsa ya kai naira 5,250.
Ana sa ran fara karɓar buƙatun sayen hannayen jarin daga ranar 14 ga Satumba zuwa 13 ga Oktoba 2026.
Bayan kammala wannan wa’adi, za a tantance buƙatun masu zuba jari sannan a sanar da su adadin hannayen jarin da suka samu.
Haka kuma, neman wani adadi na hannayen jari ba ya tabbatar da cewa mutum zai samu duk adadin da ya nema, musamman idan buƙatun suka yi yawa fiye da adadin hannayen jarin da ake da su.
Ana kuma sa ran za a sanya hannayen jarin Matatar Dangote a babban kasuwar hannayen jari ta Najeriya, inda daga nan farashinsu zai riƙa canzawa bisa buƙata da kuma yanayin kasuwa.
Kuɗaɗen da za a samu daga wannan IPO na daga cikin abubuwan da ake sa ran za su taimaka wajen faɗaɗa ayyukan matatar, wadda ke shirin ƙara ƙarfin tace man daga kusan ganga 650,000 zuwa 700,000 a rana, zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana.
