Dan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar ADP, Amb. Aliyu Bin Abbas, ya taya al’ummar Musulmi na Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar zagayowar Eid-el-Kabir, tare da yin kira ga jama’a da su gudanar da shagulgulan Sallah cikin lumana da bin doka.
A cikin saƙon taya murnar Sallar da ya aikewa manema labarai, Amb. Aliyu Bin Abbas ya bukaci al’umma da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa haɗin kai, ƙaunar juna da taimaka wa marasa galihu domin ƙara inganta zamantakewar al’umma.
Ya ce koyarwar babbar Sallah tana nuna muhimmancin haƙuri, biyayya da sadaukarwa, don haka ya kamata Musulmi su ci gaba da rungumar kyawawan ɗabi’u domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Dan takarar shugaban ƙasar ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya a Najeriya, yana mai kira ga jama’a da su guji duk wani abu da ka iya haddasa rikici ko barazana ga tsaron al’umma yayin gudanar da bukukuwan Sallah.
Haka kuma, Amb. Aliyu Bin Abbas ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya, Ya magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki, tare da bai wa shugabanni hikima da adalci wajen gudanar da harkokin mulki.
Ya kuma yi fatan Allah Ya karɓi ibadu da layyukan al’ummar Musulmi tare da maimaita wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya, yalwar arziki da zaman lafiya.
