Dan Majalisar Wakilan Najeriya,mai wakilatar Kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada Hon.Alhassan Ado Doguwa, ya musanta zargin da ake yadawa cewa yana shan wani abu mai kama da kwaya dake gusar da hankali.
Doguwa ya bayyana hakan ne a hirarsa da DCL Hausa, bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta.
Ya kara dacewa sharri aka yi masa aka ce kwaya ce a bakinsa, in da yace alawa ce da kowa zai iya sha.
Dan majalisar ya ce masu yada wannan zargi na kokarin bata masa suna ne a idon jama’a.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta.
