Babban daraktan hukumar kula da taswirar filaye da kasa da kuma daukar bayanai ta jihar Kano (KANGIS) Dr. Dalhatu Sani Aliyu yace ranar da aka tsayar na kammala sabunta takardun filaye da gidaje a jihar Kano na nan daram.
Gwamnatin jihar Kano ta tsayar da ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2025 domin dakatar da sabunta takardun mallakar fili ko gida a Kano.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 2024 kwamishinan kasa na Kano Alhaji Abduljabbar Umar Muhammad Garko ya bayyana matsayin gwamnatin Kano kan wa’adin da aka tsayar na sabunta takardun mallakar kadarori na gida da filaye da kafi sani da C -Of -O.
A yayinda yake zantawa da TST Hausa a ofishinsa,ranar Alhamis, Daraktan hukumar ta KANGIS Dr.Dalhatu Aliyu yace daga ranar Juma’a 31 ga watan Janairun 2025 an dakatar da aikin sabunta takardun mallakar fili ko gida a Kano.
“Sabunta takardun na da matukar mahimmaci ko bayan ran mutum,kuma fili ko gida yana daraja ne idan aka sabunta masa takardu, kamar gata mukayi mutum ,sanan za’a rage rugingimu na mallakar kadarori ” Inji Dr.Dalhatu.
Yace zuwa yanzu mutane masu tarin yawa sun bada hadin Kai a cikin kwana 45 da fara aikin.
Ya kara da cewa har yanzu akwai sauran dama ga wadanda basuyi ba , yana mai cewa komai zai iya faruwa da fili ko gidajen da ba’a sabuntawa takardun mallakar na C -Of-O ba.
Amma har Yanzu gwamnati bata yanke matakin da zata dauka ga wadanda suka gaza yin biyayya ga umarnin ba, acewar Daraktan.
Ya shaida cewa ,nan gaba za’a fitar da adadin sunayen mutanan da suka sabunta takardunsu a hukumar ta KANGIS.