Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tare da jiga jigai a ADC sun gudanar da zanga-zanga zuwa hedikwatar hukumar INEC a Abuja, domin nuna rashin jin dadinsu kan abin da suka kira tauye hakkinsu a cikin jam’iyyar ADC.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa akwai zargin katsalandan da kuma rashin adalci a cikin harkokin shugabancin jam’iyyar ADC, lamarin da suka ce yana hana wasu bangarori damar gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
Atiku Abubakar ya ce sun je INEC ne domin neman hukumar ta sa baki cikin lamarin, tare da tabbatar da cewa an bi doka da ka’idojin jam’iyya wajen tafiyar da harkokin ta.
Ya kara da cewa, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, rikicin na iya yin illa ga dimokuradiyya da kuma hadin kan ‘yan siyasa a kasar.
Masu zanga-zangar sun kuma bukaci INEC da ta yi cikakken bincike kan rikicin da ke addabar ADC, tare da daukar matakin da ya dace domin dawo da zaman lafiya da adalci a jam’iyyar.
A yayin zanga-zangar, jami’an tsaro sun kasance a wurin domin tabbatar da zaman lafiya, inda aka gudanar da komai cikin lumana ba tare da samun wata hatsaniya ba.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun sabani tsakanin bangarori daban-daban a cikin ADC, wanda ke janyo cece-kuce a fagen siyasar Najeriya.
Zuwa yanzu rikicin shugabanci a ADC din na gaban kotu, a yayinda kuma ake cigaba da samun billar rigin gimu.
TST Hausa ta rawaito cewa daga cikin masu zanga zangar harda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar da Aminu Waziri Tambuwal da Peter Obi da Raouf Aregbesola da Dino Malaye da sauransu
