Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta gudanar da aikin koyar da aikin hajji a aikace ga maniyyatan Kano aikin domin tabbatar da sun fahimci muhimman rukunan aikin Hajji kafin tafiya ƙasa mai tsarki.
Koyar da aikin wanda ya gudana a sansanin Alhazai ya haɗa da koyar da alhazai yadda ake sanya harami,da gudanar da ɗawafi a Ka’aba, yin Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa, tsayuwar Arfa, kwana a Muzdalifa da Mina, tare da yadda ake jifar jamarori kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A jawabin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda Mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo ya wakilta,Gwamnan ta nemi mahajjatan da su girmama dokokin kasar Saudiyya.
Murtala Sule Garo ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da jin daɗi da walwalar alhazan jihar yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Ya ce tuni gwamnan jihar Kano ya amince da baiwa kowanne maniyaci kyautar Riyal 200 da Hirami domin kyautata musu.
Ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da tallafa wa hukumar alhazai tare da samar da duk abin da ake buƙata domin tabbatar da alhazan jihar sun gudanar da ibadunsu cikin sauƙi da kwanciyar hankali.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle ya bayyana cewa an shirya horaswar ne domin bai wa maniyyata cikakkiyar fahimta kan yadda ake gudanar da aikin Hajji yadda ya kamata.
Ya kuma tabbatar dace babu wani mahajjaci da bai samu Visa ba a Kano.
Ya ce hukumar ta samar da malamai da jami’ai masu ƙwarewa domin jagorantar alhazai tare da wayar musu kai kan muhimmancin bin dokoki, haƙuri da haɗin kai a lokacin aikin Hajji.
Malaman addini da jami’an hukumar sun kuma yi amfani da misalai da kwaikwayo wajen bai wa maniyyatan cikakkiyar fahimta kan yadda ake gudanar da aikin Hajji tare da gujewa kura-kurai da ka iya tasowa yayin gudanar da ibadar.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana jin daɗinsu kan yadda aka shirya horaswar, suna masu cewa hakan ya ƙara musu ilimi da kwarin gwiwa kafin tafiya ƙasar Saudiyya.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta kuma buƙaci alhazai su kasance masu haƙuri, biyayya da kiyaye dokokin ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.
